Hungary ta zargi Croatia da fasa kaurin mutane

'Yan gudun hijra

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

'Yan gudun hijra

Hungary ta zargi makwabciyarta Croatia da taka dokokin kasa da kasa wajen hada baki ana fasa kaurin mutane bayan da Croatian ta fara mayar da 'yan gudun hijra zuwa Hungary din ba tare da anyi musu rijista ba.

Mai magana da yawun Gwamnatin hungary Zoltan Kovacs ya bayyana cewa wani jirgin kasa ya iso Hungary dauke da 'yan gudun hijra fiye da dubu guda da kuma jami'an 'yan sandan Croatia 40 a cikin sa, wannan mataki ne na taka dokokin kasa da kasa.

Firayi Ministan Kuroshiya Zoran Milanovic ya gargadi 'yan gudun hijira da ke tururuwa zuwa kasar da cewa zai kora su, domin a cewar sa, kasar ba za ta zama "matattarar su ba".

Shugaban ya ce kasar sa ba za ta rufe kan iyakar ta gaba daya ba, amma ta daina karbar karin 'yan gudun hijira.

Jawabin Milanovic na zuwa ne a lokacin da Kuroshiya ta rufe bakwai daga cikin hanyoyi takwas da 'yan gudun hijira ke bi wurin shiga kasar a kan hanyar su ta shiga Turai.

Sama da mutane 14,000 ne suka shiga Kuroshiya a galabaice kuma cikin matsanancin hali.