'Yan gudun hijra dubu 10 sun isa Austria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan gudun hijra

Mahukunta a Austria sun ce sun yi amanna cewa kimanin 'yan gudun hijra dubu 10 sun isa kasar a cikin sa'oi 24.

Mafi yawa daga cikin su, mahukuntan Hungary ne su ka kai su bayan da su ka shiga kasar ta cikin makwabciyarta Croatia.

Hungary dai ta cigaba da sukar Croatia inda ta ke zarginta da taka dokokin kan iyaka.

Ministan harkokin wajen Hungary Peter Szijjarto ya bayyana cewa a bayyane ta ke karara cewa gwamnatin Croatia ta taka dokokin kungiyar tarayyar turai.

Mr Szijjarto ya ci gaba da cewa maimakon Croatia ta bawa masu gudun hijra mafakar da ta dace, sai ta tura su zuwa kasar mu.