Mutane 54 sun mutu a harin Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AP

Hukumomi a Najeriya sun ce kimanin mutane 54 ne suka mutu a hare-haren bama-bamai guda uku a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Babban jami'in hukumar bayar da agajin gaggawa, NEMA a yankin arewa maso gabashin kasar, Muhammad Kanar, wanda ya tabbatar wa BBC da alkaluman, ya kara da cewa kimanin mutane casa'in da shida ne suka jikkata.

Ya kara da cewa an kai mutanen da suka jikkata asibiti domin ceto rayukansu.

Ganau sun shaida wa BBC cewa bama-baman sun tashi ne da misalin karfe 7:40 na daren ranar Lahadi a kusa da masallaci da kuma sinima.

Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin dana bama-baman, ko da ya ke Boko Haram ta sha kai hare-hare a birnin.

Tun bayan da aka rantsar da Shugaba Buhari a matsayin shugaban Nigeria a watan Mayu, 'yan Boko Haram sun hallaka mutane fiye da 1,000.

Karin bayani