An kai harin kunar bakin wake Kamaru

Wani hari da mayakan BH suka kai Kamaru Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Jamhuriyar Kamaru na daga cikin kasashe makoftan Nigeria da mayakan BH suka addaba.

Akallah mutane 5 sun rasa rayukansu a wani harin kunar bakin wake da aka kai arewacin jamhuriyar Kamaru.

Cikin wadanda suka rasun har da jami'in 'yan sanda, da wasu fararen hula 2 ka na da 'yan kunar bakin waken mata su 2 da suka tashi bam din da ke daure a jikinsu, a lokacin da jami'an tsaro suka tsaida su a kusa da kofar shiga garin Mora da ke arewacin kasar.

Mayakan BH dai sun zafafa kai hare-hare ba ma cikin Nigeria kadai ba, har ma da kasashe makofta irin jamhuriyar Kamaru tun bayan da kasar ta shiga cikin yakin da ake yi dan ganin bayan kungiyar masu ikirarin kafa daular musuluncin.