An cire manhajar goge talla daga intanet

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana amfani da wannan manhajar ne wajen gurbata tallace-tallacen da ke intanet

Marco Arment wanda daya ne daga cikin mutanen da suka shahara wajen fito da manhajar canja ko goge tallace-tallacen mutane ya janye manhajar tasa daga rumbun samun manhajojin intanet.

Ya ce " cimma irin wannan nasara ba wani abun alfahari ba ne".

Mista Marco wanda na daya daga cikin gamayyar mutanen da suka kirkiri manhajar Tumblr, ya kirkiri manhajar Peace, wadda take goge ko kuma ta gurbata fasalin tallace-tallace da masu haja suka sanya a shafukan intanet.

Ita dai wannan manhaja ta Peace tana aiki ne a kan fasahar intanet ta iOS9 wanda shi ne sabon tsarin da wayar iPhone take amfani da shi.

Manhajar mai darajar dala 2.99 ta yi tashin gwauron zabi dare daya kuma tana tafiya kafada da kafada wasu manhajojin irin su Purify da Crystal.

Shi dai mista Arment wanda harwayau shi ne mutumin da ya kirkiro da manhajar Instapaper ya ce manhajar tasa ta goge tallace-tallace ta Peace ta kara wa fasahar yawo a intanet ta iOS sirri da kuma saurin zagayawa a duniyar gizo.

Ya kuma kara da cewa ta ita wannan manhaja ta Peace, ana iya satar bayanai da zuke cajin batirin wayoyin mutane ba tare da yardarsu ba.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana kuma satar bayanan sirri da ita.

Sai dai kuma mutane da yawa sun yi kakkausan suka ga manhajar ta goge tallace-tallace bisa biyan kudi da masu son goge ko kuma gurbata tallan masu haja, suke yi.