Ba ni da hannu a shari'ar Saraki - Buhari

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tun bayan da aka rantsar da Sanata Saraki, ya ke fuskantar kalubale

Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya ce ba shi da hannu a shari'ar da ake yi wa shugaban majalisar dattawan kasar, Abubakar Bukola Saraki a kan zargin yin karya wajen bayyana dukiyarsa.

Kakakin shugaban kasar, Garba Shehu a cikin wata sanarwa, ya ce shari'ar da ake yi wa Sanata Saraki tsari ne na shari'a wanda bai shafi fadar shugaban kasar ba.

"Kundin tsarin mulki ne ya kafa wannan kotun a don haka wannan batun tsarin shari'a ne wanda babu hannun fadar shugaban kasa," in ji Shehu.

Jam'iyyar adawa ta PDP ta zargi shugaba Buhari a kan cewar makarmashiya yake yi domin a tsige Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar dattijai.

A ranar Juma'a ce kotun kula da da'ar ma'aikata ta ba da sammacin kama Sanata Saraki saboda kin bayyana a gaban kotun domin ya kare kansa bisa zargin ya saba ka'ida a wajen bayyana abin da ya mallaka bisa tsarin dokar kasar.

Kotun na zargin Saraki da aikata laifuka goma sha uku wadanda ke da alaka da zargin boye wasu daga cikin kadarorin da ya mallaka.

Sai dai Bukola Saraki ya musanta dukkanin zarge-zargen.