Zan amsa gayyatar kotu — Saraki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Saraki ya ce zai gurfana a gaban kotun domin wanke kansa daga zargi.

Shugaban Majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya ce zai gurfana a gaban kotun kula da da'ar ma'aikata ranar Talata.

Saraki, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai, ya kara da cewa zai yi hakan ne bayan shawarwarin da lauyoyinsa suka ba shi na zuwa kotun domin wanke kan sa daga zargin da ake yi masa.

Kotun dai tana zargin sa ne da laifuka goma sha uku, wadanda ke da alaka da kin bayyana kadarorinsa yadda ya kamata a lokacin da yake gwamnan jihar Kwara.

Shugaban Majalisar dattawan ya kara da cewa zai je gaban kotun ne a matsayin na wanda yake biyayya ga dokokin kasar.

A baya dai Bukola Saraki ya ki gurfana a gaban kotun, yana mai cewa ba zai yi hakan ba saboda ya kai karar ta wata babbar kotun Abuja wacce ta bayar da umarni a dakatar da gurfanar da shi.

Kotun ta kula da da'ar ma'aikata dai ta bai wa Babban Sufeton 'yan sandan kasar ya kai mata Mr Saraki ranar Talata idan har ya ki mutunta umarninta.