Sauye-sauyen tattalin arzikin China

Tashar watsa labaran BBC ta yi labari a kan bunkasar tattalin arzikin China da kuma yadda ake samun bunkasar birane a kasar; da kuma hotuna da bidiyon da aka dauka na ci gaban tattalin arzikin kasar.

Habakar tattalin arzikin China ta jawo bunkasar birane tare da yin sanadin komawar miliyoyin wadanda suke aiki a kauyuka zuwa birane domin neman aiki.

Ga hotuna da bidiyo kan labarin irin gagaruman sauye-sauyen da China ta samu.

Bayanan da Majalisar Dinkin Duniya ta tattaro sun nuna cewa yawan biranen da ke China masu yawan mutane miliyan daya ko fiye da haka sun karu daga 16 a shekarar 1976 zuwa 106 a shekarar 2015. Idan aka kwatanta wannan adadi za a ga ya ninka na Amurka wadda take da birane 45 da kuma Turai mai birane 55.

'Bunkasar gine-gine'

Kwararar mutane daga kauyuka zuwa birane a China ta samo asali ne daga irin yadda ake samun habakar gine-gine.

Yaya aka yi China ta habaka harkar gine-ginenta nan da nan? To ga dai wani misali na wani dogon gini da aka yi cikin kwanaki tara kacal.

Amma duk da cewar ana gina gidaje sosai, hakan ba ya nufin mutane na zama a cikinsu, mafi yawan sababbin garuruwan da aka gina babu kowa a cikinsu, har ma ana yi musu lakabi da "Kufai."

'Ranaku masu hazo'

Bunkasar tattalin arzikin China ya zama barazana ga bangaren muhalli inda gurbatar yanayi ya ta'azzara saboda yawan amfani da makamashin gawayi a tasoshin samar da wutar lantarki, wanda China ta dogara da shi domin samar da makamashi.

Hoton da aka dauka da kamarar tauraron dan adam na yadda hazo ya gurbata yanayin wata rana a Beijing a shekarar 2013.

Hotunan da tauraron dan adam ya dauka na birnin Beijin sun nuna yadda hazo da dusar kankara suka gurbata yanayi a watan Janairun 2013 - hoton da ke dama na nuna yadda hazo mai launin fari-fari da ruwan kasa ya mamaye samaniyar birnin.

China na kokarin rage gurbatar yanayi tare da rufe dubban masana'antun da ke amfani da makamashin gawayi.

Kazalika, a cewar ma'aikatar muhalli, takwas ne kacal daga cikin birane 74 na manyan biranen kasar suka cimma dokokin gwamnati na ingantaccen matsayi a shekarar 2014.

Alal misali, an yi la'akari cewa iskar da ake shaka a bangaren da ofishin jakadancin Amurka da ke Beijing yake, gurbatacciya ce wacce za ta iya jawo cututtuka, kuma ba ta yi daidai da tsarin da Amurka ta sa na ingantacciyar iska ba a mafi yawan lokuta, duk da cewa mafi yawan ranakun da ake ganin iskar da ake shaka na jawo cututtuka sun ragu tun shekarar 2008, lokacin da ofishin jakadancin ya fara tattara bayanai.

China ta fara fitar da ka'idoji kan ingantacciyar iskar da ake shaka a shekara ta 2012.

Ta ce takaita fitar da hayakin masana'antu da kuma rufe ma'aikatun da suke amfani da makamashin gawayi ya taimaka wajen rage gurbatacciyar iska a shekarar 2015.

'Bunkasar arziki'

Jam'iyyar Kwaminisanci ta fara gabatar da kasuwar 'yan jari hujja a shekarar 1978. Bayan da aka bude kasuwar hannayen jari ta kasashen waje a shekarar 1980, China ta zama ja-gaba wajen samar da kayayyaki saboda masana'antu sun yi amfani da damar biyan masu aikin karfi kudi kalilan.

Tattalin arzikin China ya habaka da kashi 10 cikin 100 a duk shekara daya cikin shekaru 30 a jere har zuwa shekara ta 2010, duk da cewa bunkasar tattalin arzikin ya ja baya tun tuni.

A shekarun baya-bayan nan ta wuce Japan inda ta zamo kasa mafi karfin tattalin arziki ta biyu a duniya, duk da cewa ma'aunin arzikinta na shekara-shekara GDP, bai kai na Amurka da Japan da Jamus da kuma Biritaniya ba.

'Yawon shakatawa'

GDP din China yana tafiya ne da hauhawar kudin shiga ya ta'allaka ne da karuwar yadda mutane suke samun kudin shiga - China ita ce kasar da tafi kowacce samun yawan 'yan bude ido, kuma bakinta su ne na farko a duniya da suka fi kashe kudi, inda ake kashe kimanin dala biliyan 165 domin zuwa hutu.

Kasashen da suka fi shahara sun hada da Hong Kong da Japan da Faransa da Korea ta kudu da Amurka da kuma Thailand.

'Kwashe aladu'

Naman alade shi ne naman da mutanen China suka fi so tun da jimawa, amma marasa galihu sun dauke shi a matsayin abinci mai daraja da ake amfani da shi a ranaku na musamman kawai.

Ba kamar da ba. Ganin yadda kashe kudin da al'umma ke yi ya karu, yawan masu cin naman alade ya karu, kuma yanzu China ce cin rabin aladun da ake ci a duniya.

Tuna baya?

Duk da karuwar kudaden shiga da mutane ke samu, wasu ba su amfana kamar sauran ba - akwai bambanci sosai a ratar da ke tsakanin kudaden shigar da mutanen kauye da na birni ke samu tun daga shekarar 1990.

Hanyar yin rijistar al'ummar China da aka fi sani da "hukou", ta munana bambancin, saboda ta hana yawancin ma'aikata 'yan ci rani samun damar ta hanyar lafiya da gidaje da walwala a biranen da suke aiki.

Kuma yawan kaurace-kaurace zuwa birane ya shafi yara da dama- China tana da yara kimanin miliyan 61 da suke rayuwa a kauyuka ba tare da iyayensu ba.

Wadanda suka tsara wannan jadawali da shafin su ne Christine Jeavans da Salim Qurashi da James Offer da Helier Cheung da kuma Marcelo Zanni.