Wasu 'yan kungiyar IS sun juya mata baya

Hakkin mallakar hoto IS
Image caption Mayakan IS sun kama yankuna da dama a Syria da Iraki

Wani nazari da aka yi na ra'ayoyin wasu tsaffin mayakan kungiyar IS kusan su sittin ya nuna abin da ya sa suka dawo daga rakiyarta.

Binciken wanda jami'ar King's College ta Landan ta gudanar, ya gano cewa babban dalilin shi ne na rashin jituwa tsakanin bangarorin masu jihadin.

Wasu daga cikin wadanda suka fuce daga kungiyar basu yadda da zalincin da kungiyar IS ke yi wa musulmai mabiya shi'a ba.

Wasunsu kuma na takaicin rayuwa karkashin dokokin IS, wanda ya saba da farfaganda kungiyar.

Yayin da wasu kuma mutane biyu ke cewa sun fita daga kungiyar IS din ne bayan da suka samu labarin cewa za'a sa su kai harin kunar bakin wake.