Kamfanin SNCF na Faransa ya nuna bambamci

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kotu ta samu kamfanin da laifuka tara cikin goma

An umurci Kamfanin jiragen kasa na Gwamnatin Faransa da ya biya kudi Euro kusan dubu 200 - ga kowane daga cikin ma'aikata 800 'yan asalin kasar Morocco.

Hakan ya biyo bayan bambancin da aka nuna wa ma'aikata saboda kasar da suka fito.

Wata kotun kwadago a Paris ta ce kamata yayi mutanen su kasance da 'yancin yanayin aiki da fansho iri guda da takwarorinsu na Faransa.

Kotun ta ce kamfanin SNCF ya takaita ci gaban ma'aikatan kuma ana ba Faransawa da ke aiki tare da su fifiko a kan 'yan Morocco.

An samu kamfanin da laifuka tara cikin goman da daruruwan ma'aikatan suka shigar.

Kowane ma'aikaci zai samu sama da dala dubu dari biyu.

Kamfanin na SNCF na da wata daya da zai iya daukaka kara.