Wa'adin kama Bukola Saraki zai cika

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Majalisar Dattijai a Najeria Bukola Saraki

A Najeriya, a ranar Litinin ne wa'adin sammacin kamo Shugaban Majalisar Dattawan kasar Sanata Bukola Saraki da kuma gurfanar da shi a gaban kotun ke cika.

A ranar Jumu'a ne Sanata Saraki ya garzaya kotun daukaka kara da ke Abuja, babban birnin kasar domin kalubalantar umarnin da hukumar kula da da'ar ma'aikata ta bayar a kama shi.

Hukumar na zargin Saraki da aikata laifuka goma sha uku wadanda ke da alaka da zargin boye wasu daga cikin kadarorin da ya mallaka.

Sai dai Bukola Saraki ya musanta dukkanin zarge-zargen.

'Yan Najeriya sun zuba ido su ga yadda wannan dambarwa za ta kaya tsakanin shugaban Majalisar Dattijan da kuma rundunar 'yan sandan kasar.