'Ya kamata Assad ya fuskanci shari'a'

Hakkin mallakar hoto syria army
Image caption Syria ta daidai ce saboda yaki

Wata babbar jami'ar a hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Carla del Ponte, ta ce ya kamata shugaba Bashar al-Assad ya fuskanci shari'a ko da ya ci gaba da kasancewa a kan mulki.

Da take magana da anema labarai, Ms Ponte ta tuno da abin da ya faru da tsohon shugaban kasar Serbia da Yugoslvia, Slobodan Milosvic.

Wanda ya ci gaba da mulki bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya a tsohuwar tarayyar Yugoslavia amma duk da haka ya fuskanci shari'a a Hague.

Ms del Ponte ta ce hakan na iya faruwa da Mr al-Assad.

Ita dai mamba ce a hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke gudanar da bincike kan take hakkin bil adama a Syria wadda kuma ta rubuta sunayen mutanan da ake zargi da hannu a ciki.