Jam'iyyar Syriza ta dawo mulki a Girka

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jam'iyyar dai ta samu nasarar lashe kujerun majalisa fiye da rabi

Jam'iyyar Syriza ta 'yan gurguzu wacce Firai Ministan Girka, Alexis Tsipras ke ciki, ta samu nasarar dawo wa kan mulkin kasar bayan da ta lashe babban zaben kasar karo na biyu a wannan shekarar.

Sai dai bisa la'akari da mafi yawancin kuri'un da aka kidaya, zai yi wuya jam'iyyar ta samu isassun kujeru a majalisar dokoki da za su ba ta damar kafa gwamnati ba tare da hada gwiwa da jam'iyyar masu ra'ayin 'yan mazan jiya ba.

Tuni dai Alexis Tsipras ya tabbatar da cewa zai hada gwiwa da jam'iyyar masu ra'ayin 'yan mazan jiya, wadanda da su ne ya yi gwamnatin hadaka a baya.

Ya fada wa taron jama'a masu murnar cin zaben a babban birnin kasar na Athens cewa sakamakon ya bai wa jam'iyyar ta Syriza sabuwar damar canza abubuwan da suka hana kasar ta ci gaba.

Wata mai magana da yawun jam'iyyar ta Syriza ta ce gwamnatin za ta zartar da yarjejeniyar da aka cimma a kan shirin ceton kasar da kasashen da suke bin Girkar bashi.

Sai dai ta ce za a kai ruwa rana a kan batun bashin da ake bin kasar.