'Boko Haram ta mamaye kauyukan Monguno'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rikicin Boko Haram ya daidaita jihar Borno

Bayanai daga jihar Borno sun nuna cewar mayakan Boko Haram sun mamaye galibin kauyukan da ke kewaye da garin Monguno.

Wani dan civilian JTF ya shaidawa BBC cewar ko a karshen wannan makon ma 'yan Boko Haram sun halaka mutane talatin da biyu, kuma sun jikkata wasu mutanen ashirin da tara a harin kunar bakin wake.

Dan civilian JTF din ya ce "Yanzu haka akwai 'yan Boko Haram a Gonari, akwai su jibiwa, akwai su a Masara, akwai su gratiri, Krenuwa, ciki-gudu, garna, kwatar mai shayi, arimisuku, duk suna cikin kauyukan nan."

"Kullum suna fitowa bakin hanya suna yi wa mutane fashi in sun debo kaya daga Maiduguri, kuma su yanka mutum," in ji dan civilian JTF din.

Ya kara da cewar akwai jami'an tsaro a cikin garin Monguno sai dai babu su a kan hanya ko kuma a kauyukan da ke kusa da garin.

Ko a ranar Lahadi ma sai dai kimanin mutane 54 ne suka mutu a hare-haren bama-bamai guda uku a Maiduguri.

Tun bayan da aka rantsar da Shugaba Buhari a matsayin shugaban Nigeria a watan Mayu, 'yan Boko Haram sun hallaka mutane fiye da 1,000.