Sojin Burkina Faso sun ki mika mulki

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Janar Diendere ya bukaci a yi wa sojin da suka yi juyin mulki afuwa.

Shugaban sojojin da suka yi juyin mulki a Burkina Faso ya ki mika mulki duk da wa'adin da aka dibar masa na ranar Talata da safe domin ya mika mulkin.

Janar Gilbert Diendere ya ce idan sojin kasar suka kai musu hari, to za su rama.

Rundunar sojin kasar dai ta bukaci mutanen da ke zanga-zangar kyamar juyin mulkin a Ouagadougou, babban birnin kasar da su koma gida, a daidai lokacin da ake fargabar barkewar rikici.

A makon jiya ne Janar Diendere ya jagoranci sojin da ke kula da fadar shugaban kasa wajen kwace mulki daga hannun gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin Michel Kafando.

Rundunar sojin kasar dai ta aika dakarunta babban birnin kasar domin kwace iko daga hannun dakarun fadar shugaban kasar idan wa'adin da aka dibar musu ya cika ba tare da sun mika wuya ba.

Kungiyar Tarayyar Turai da ta takwararta ta kasashen Afirka da kasashen Amurka da Faransa sun yi Alla-wadai da juyin mulkin.