Wakilan ECOWAS za su je Burkina Faso

Image caption Wasu daga cikin shugabannin kasashen ECOWAS

Shugabanni kasashen Afrika 6 da suka hada da na Najeriya da Togo da Senegal da Benin za su isa Burkina Faso ranar Laraban nan domin mayar da shugaban riko na kasar Michel Kafando kan kujerarsa.

A ranar Talata ne shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS, a wani taro da suka gudanar a Najeria, suka yanke shawarar tura tawagar kungiyar domin mayar da gwamnatin ta farar hula kan mulki.

A wajen taron a ranar Talata, shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS sun yi Allah wadai ga juyin mulkin da sojoji suka yi a Burkina Faso, sannan suka bukaci sojojin da su mika mulki ba tare da gindaya wani sharadi ba.

Tun da farko, madugun juyin mulkin, Janar Gilbert Diendere, wanda ya bukaci a yafewa sojojin da suka yi juyin mulkin, ya ce yana jiran sakamakon taron kungiyar.

Sai dai bisa duk kan alamu shugabannin kungiyar ta ECOWAS ba su amince da bukatarsa ba ta neman a yafewa sojojin da suka yi juyin mulkin.