An gargadi EU kan 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban 'yan gudun hijirar Syria suna cikin tsaka mai wuya

Hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa shirin tarayyar Turai na sake tsugunnar da dubban 'yan gudun hijira ba zai isa ba wajen shawo kan matsalar da ake ciki a yanzu.

Wata kakakin hukumar, Melissa Fleming, ta yi kira ga Tarayyar Turai da ta kafa isassun wuraren karbar 'yan gudun hijirar musamman a kasar Girka.

Tana magana ne gabanin wani taro da kungiyar tarayyar Turan za ta yi nan gaba kadan a Brussels inda za ta tattauna a kan sake rarraba 'yan gudun hijirar.

A waje daya kuma kasar Hungary ta gargadi 'yan gudun hijirar da kada su taba shingen wayar da ta like kan iyakokinta da Serbia, tana mai cewa za su iya jin mugun rauni.

Haka kuma kungiyoyin agaji da ke aiki a tsibirin Lesbos na kasar Girka sun ce tsakanin 'yan gudun hijira dubu uku zuwa dubu biyar ne ke isa wajan a kullum.

Rahotannin na cewa Iska da ruwan sama mai karfi na saka tafiyar da ake yi daga Turkiyya a cikin jirgin ruwa mai hadarin gaske.