Mahajjata sun soma aikin hajji

Hakkin mallakar hoto none
Image caption Filin Arfa a Mna.

Dubun dubatar mahajjanta bana daga dukkan sassan duniya sun soma aikin Hajji a kasar Saudiyya.

Aikin Hajji dai daya ne daga cikin shika-shikan musulunci, kuma bana ana sa ran mutane fiye da miliyan biyu ne za su yi wannan aikin na ibada.

Shirin aikin hajjin na bana dai ya fuskanci kalubale yayin da wani hatsari a Masallacin harami a Makka lamarin da janyo rasuwar mutane fiye da 100.

Maniyata daga kasar Indonesia su ne suka fi na kowacce kasa yawa inda suka kai su 168,000.

Yanzu haka dai bayanai sun ce mahajjata miliyan daya da dubu dari hudu sun riga sun isa Muna.

An tanadi rumfuna kimanin dubu 160 wadanda wuta ba za ta iya cin su ba a Muna.

Hawan Arfa shi ne kololuwa a aikin hajji kuma a ranar Laraba ne mahajjatan za su yi shi.

A bana, hukumomi a Saudiya sun yi gargadin za a iya samun yanayi mai zafi da kuma ruwan sama mai dauke da iska mai karfin gaske.