Skype ya ci gaba da aiki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu amfani da manahajar ba sa iya kiran mutane

Manhajar Skype ta ci gaba da aiki bayan ta kwashe tsawon lokaci tana fuskantar matsala sakamakon matsalar intanet.

Matsalar dai ta fara ne a Biritaniya ranar Litinin da misalin karfe 09:00 na safe.

Wata sanarwa da kamfanin Microsoft ya fitar ta ce matsalar ta shafi dukkan bayanan mutanen da ke amfani da manhajar.

Sanarwar ta ce, "an gano matsala game da yadda masu mu'amala da shafin ke yin kiran abokansu".

Manhajar ta ci gaba da aiki da tsakar daren Talata.

Matsalar dai ta sa mutane da dama ba sa iya ganin wadanda za su kira ko da kuwa mutanen suna kan layukansu.

Masu amfani da Skype daga kasar Birtaniya da Australia da Japan sun sanar da fuskantar matsalar.

Hakan ya sa masu amfani da manhajar sun kasa yin kira ko kuma tattaunawa ta gani-ga-ka.

Ma'aikatan Skype din sun yarda da faruwar matsalar a shafin twitter.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mutane daga kasashe daban-daban sun koka dangane da daukewar Skype din

Kamfanin ya kuma nemi afuwar masu amfani da Skype din dangane da matsalar da aka samu.