Skype ya dauke daga intanet

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu amfani da manahajar ba sa iya kiran mutane

Manhajar Skype ya dauke daga intanet kuma mutane da dama ba za su iya yin amfani da fasahar ba.

Matsalar dai ta fara ne a Birtaniya ranar Litinin da misalin karfe 09:00 na kasar.

Kuma sakamakon hakan masu amfani da manhajar sun kasa yin kira ko kuma tattaunawa ta gani-ga-ka.

Wata sanarwa da kamfanin Microsoft ya fitar ta ce matsalar ta shafi dukkan bayanan mutanen da ke amfani da manhajar.

Yanzu haka dai masu amfani da Skype din daga kasar Birtaniya da Australia da Japan sun sanar da fuskantar matsalar.

Ma'aikatan Skype din sun yarda da faruwar matsalar a shafin twitter, a inda kuma suka fadi cewa suna kokarin gyara matsalar cikin gaggawa.

Bugu da kari, a wata sanarwa mai tsayi, kamfanin ya ce matsalar ba ta shafi Skype da ke kan shafin intanet ba, wanda za a iya yin amfani wajen yin kira da kuma aika sakonnin gaggawa.

Sanarwar ta kara da cewa ma'aikatan kamfanin suna kan aiki ka'in-da-na'in don ganin sun sake sada masu amfani da Skype din.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mutane daga kasashe daban-daban sun koka dangane da daukewar Skype din

Kamfanin ya kuma nemi afuwar masu amfani da Skype din dangane da 'yar matsalar da aka samu.