Apple ya fara cire manhaja mai cutarwa

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Wayar kamfanin Apple

Katafaren kamfanin kera kwamfutocin Apple ya ce yana daukan matakin cire wata boyayyar manhaja mai cutarwa data samu kutsawa cikin wasu manhajojin da wayoyi da kwamfutocin Apple ke amfani da su a China.

Ana ganin wannan ne babban hari na farko da kamfanin Apple ya fuskanta a rumbun manhajojinsa.

Kamfanin ya ce masu kuste sun makala boyayyar manhaja mai cutarwa a cikin manhajojin na'urorin Apple ta hanyar yaudaran masu kirkiran manhaja akan su yi amfani da manhaja mai kama da ta kamfanin Apple.

Mai magana da yawun kamfanin Apple Christine Monaghan ta ce an cire manhajojin da suka harbu daga rumbun Apple.

Ta ce "masu amfani da kwamfutocin Apple a China ne suka sauke manhajar mai cutarwa mai suna XcodeGhost akan kwamfutocin su".