An yi wa Fahmy da Baher afuwa a Masar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ma'aikatan Al Jazeera biyu ne aka yi wa afuwa

Shugaban Masar, Abdul Fattah al-sisi ya yi wa biyu daga cikin ma'aikatan gidajen talabijin na Al Jazeera uku afuwa wadanda aka samu da laifin yada labaran karya.

Mohamed Fahmy, wanda ke da takardun zama dan kasa a Canada da kuma Baher Mohamed dan Masar na daga cikin fursunoni 100 da shugaba Abdul Fattah al-Sisi ya yi wa afuwa.

Shugaban Masar din ya dauki matakin ne kwana guda kafin ya tafi birnin New York domin yin taron koli na majalisar dinkin duniya.

Dukkansu uku a watan da ya wuce ne aka yanke musu hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari.

Masu shigar da kara na gwamnati na zargin ma'aikatan Al Jazeera din da hada baki da kungiyar Muslim Brotherhood bayan an kifar da gwamnatin shugaba Mohammed Morsi a shekarar 2013.

'Yan jaridar sun musanta zargin inda suka ce suna aikinsu ne.