Rikici ya barke a yammacin kogin Jordan

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Jana'iza ce ta janyo rikicin na yau

Mummunan fada ya barke tsakanin matasan Falasdinawa da dakarun Isra'ila a birnin Hebron, na yammacin kogin Jordan.

Tashin hankalin dai ya biyo bayan jana'izar Hadeel Al Hashlamon 'yar shekaru goma sha takwas, wadda wani sojan Isra'ila ya harbe ta a wani wurin binciken ababen hawa.

Amma Falasdinawa da suka shaida lamarin sun ce, ba haka lamarin yake ba.

Masu makokin Hadeel Al Hashlamon sun yi kira ga kasashen duniya su ba da kariya, wasu kuma suka yi kiran a dau fansar abin da ya faru.

Wani bidiyo da kamfanin dillacin Falasdinawa ya nuna shi ne ya kara ruruta wutar lamarin.

Bidiyon ya nuna dalibar kwance a kasa, jini yana zuba daga jikinta, sanye da bakaken kaya da hijabi bayan wani sojan Isra'ila ya harbe ta.

Wannan lamari dai na faruwa ne yayin da zaman dar-dar ke karuwa a masallacin Al Aqsa, wurin da musulmi ke darajtashi, kuma Yahudawa ma suke girmama shi sosai.