Sojoji sun ceto mutane 241 a Borno

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Yanzu haka ana ci gaba da tantance matan da aka ceto

Rundunar sojin Nigeria ta ce dakarunta sun ceto mata da kananan yara su 241 a lokacin wani samame da suka kai kusa da garin Banki na jihar Borno.

Wata sanarwa da kakakin rundunar, Kanar Sani Usman Kukasheka ya fitar, ta ce an ceto matan ne a lokacin da dakarun suka wargaza sansanonin 'yan Boko Haram biyu da ke kauyukan Jangurori da kuma Bulatori.

Wasu daga cikin matan da aka ceto,'yan Boko Haram ne suka yi garkuwa da su ne, a yayin da wasu kuma iyalan mayakan ne.

Sanarwar ta kara da cewar dakarun sun damke mayakan Boko Haram su 43 ciki har da kwamandan kungiyar na kauyen Bulakuri mai suna Bulama Modu.

Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirarin na dakarun Nigeria din.

A farkon wannan shekarar, kungiyar Amnesty International ta yi zargin cewa mayakan Boko Haram sun sace mata da 'yan mata fiye da 2,000 tun daga watan Junairun 2014.