Sallah: Za a takaita zirga-zirga a Borno

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rundunar sojin ta ce ta dauki matakin ne domin hana Boko Haram kai hare-hare.

Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta takaita zirga-zirga a wasu yankunan jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar a lokacin bukukuwan Sallah.

Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce daga ranar Laraba, ba za a bar mutane su rika yawo a kan kekuna da babura da dokuna da kuma rakuma a Maiduguri, babban birnin jihar ba.

A cewar sanarwa, za a takaita hawa abubuwan ne daga karfe biyar na yammmacin kowacce rana.

Rundunar sojin dai ta ce ta dauki matakin ne domin dakile duk wani yunkurin kai hari na kungiyar Boko Haram.