PDP za ta iya canza sunanta

Image caption Jam'iyyar PDP ta ce za ta iya sauya sunanta

Babbar jam'iyyar adawa ta Nijeriya wato PDP, ta ce akwai yiwuwar ta sauya sunanta, a wani bangare na matakan gyare-gyare da sauya fasalinta.

Barista Abdullahi Jalo, mataimakin sakataren watsa labarai na jam'iyyar ta PDP na kasa, wanda ya sanar da hakan ya ce a kokarin kwamitin da aka kafa domin farfado da jam'iyyar, wanda Farfesa Jerry Gana ke jagoranta zai iya canja wa jam'iyyar suna idan da bukatar hakan.

Ya kara da cewa za kuma su iya gayyatar wasu jam'iyyun domin yin gamayya.

Sai dai ya ce ana samun rashin jituwa tsakanin 'yan kwamitin.

Jam'iyyar ta PDP dai ta kara shiga rudani ne tun bayan mummunan kayen da ta sha a hannun jam'iyyar APC a manyan zabukan kasar a watannin Maris da Apirilu, lokacin da mulkin PDPn na shekaru goma sha shida ya zo karshe.