Paparoma Francis na ziyara a Amurka

Hakkin mallakar hoto
Image caption Fafaroma Francis

Paparoma Francis ya isa Amurka har ya samu gaisuwa daga shugaba Obama, a ziyararsa ta farko a kasar.

Paparoman ya sauka a filin jirgi saman sojoji na Andrews ne bayan ya kammala ziyara a kasar Cuba.

A ziyarar tasa ta kwanaki shida a Amurka, Paparoma Francis zai je Washington da New York da kuma Philadelphia.

Babban Limamin Kiristan -- wanda yake burin sa mabiya darikar Katolika su kara riko da addininsu ta hanyar sakon da zai gabatar -- zai samu dandazon mutane a ganawar da zai yi a dukkan birane ukun da zai je.

Paparoma Francis -- a kan hanyar sa ta zuwa Washington -- ya shaida wa 'yan jarida cewa shi ba mai ra'ayin-rikau ba ne kamar yadda ake dauka.

Saboda tsantsanin sa, Paparoman ya ki amince wa da tayin da hukumomi a Amurka suka yi masa na a dauko shi a motar Alfarma ta Limousine.