Shugaban Volkswagen ya yi murabus

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Winterkorn ya shiga tsaka mai wuya

Shugaban kamfanin Volkswagen, Martin Winterkorn ya yi murabus, a yayin da ake ci gaba da cece-kuce game da magudin da kamfanin ya yi kan hayakin da motocinsa ke fitarwa.

A sanarwarsa ta ajiye aiki, Mr Winterkorn ya ce kamfanin Volkswagen na bukatar ya bude sabon babi.

A ranar Juma'a ake sa ran kamfanin zai sanar da sabon shugaba.

Masu shigar da kara na gwamnatin Jamus sun soma gudanar da bincike kan kamfanin bayan da aka samu korafi daga jama'a.

Ministan sufurin Jamus,Alexander Dobrindt ya musanta zargin cewa yana da masaniya kan batun cewar Volkswagen na cuwa-cuwa game da hayakin da motocinsa ke fitarwa.