Sojojin Nigeria sun kwato garin Banki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojin Najeriya sun yi ikirarin samun nasara a yakin da ta ke yi da 'yan Boko Haram a kasar.

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kame garin Banki da ke jihar Borno a arewaci maso gabashin kasar daga hannun 'yan kungiyar boko haram.

Garin na Banki na da matukar muhimmanci ta fuskar kasuwanci ga kasashen Najeriya da Kamaru da kuma Jamhuriyar Africa ta tsakiya.

Sojojin sun kuma kwace wata makaranta da 'yan kungiyar ke amfani da ita wajen koyar da yara akidarsu baya ga lalata wasu sansanoni guda 7 da kuma lalata wasu abubuwa masu fashewa da mayakan suka daddasa a tsakanin Darel da Jamal da kuma Banki kuma wasu abbama-bamai da makwabtanta ta fuskar kasuwanci.

A yayin wannan aiki, kakakkin sojojin Kanar Sani Usman Kuka Sheka ya ce sun samu tallafi daga sojojin sama na kasar da kuma sojojin kamaru.