Bam ya fashe a masallacin Idi a Yemen

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masallacin dai na mayakan Houthi ne mabiya mazhabar Shi'a

Wata majiya daga jami'an tsaron kasar Yemen ta shaida wa bbc cewa akalla mutane 25 ne suka rasa rayukansu wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da ake kyautata zaton na bom ne a masallacin idi a Sana'a, babban birnin kasar Yemen.

An ce shi wannan masallacin wanda yake kusa da wata kwalejin horas da 'yan sanda a birnin na Sana'a, yana karkashin ikon mayakan Houthi mabiya mazhabar shi'a ne.

Su dai mayakan Houthi wadanda mabiya mazhabar Shi'a ne suna yakar gwamnatin kasar ta Yemen.

Kasar Saudiyya ce kuma take jagorantar rundunar hadin gwiwa ta kasashe domin fatattakar mayakan na Houthi.