Iftila'in aikin Hajji a cikin shekaru

Hakkin mallakar hoto EPA

Wannan dai ba shi ne karon farko ba, da aka fuskanci turmutsutsu da ya halaka jama'a da dama yayin aikin Hajji.

  • A shekarar 1987, mutane 402 ne suka rasu a kokarin jami'an tsaro na tarwatsa Iraniyawa masu zanga-zangar kin jinin Amurka.

  • A lokacin aikin Hajjin shekarar 1990, mahajjata yawancinsu 'yan kasar Malaysia, su 1,426 ne suka halaka yayin wani cinkoso da aka fuskanta a wata hanya da ta ratsa dutse a kan hanyar zuwa Makkah. A lokacin hukumomin Saudiyya sun ce, yawancin wadanda suka mutu, sun halaka ne sakamakon lalacewar na'urorin da ke shigar da iska cikin hanyar ta da ratsa cikin dutse.

  • A lokacin aikin Hajjin shekarar 1998, kuma mahajjata 118 ne suka mutu a lokacin jifan shaidan, kuma yawancin wadanda suka mutu sun fito ne daga kasashen Indonesia, da kuma Malaysia. Kuma yawanci sun mutu ne sakamakon hatsaniyar da ta barke yayin da wasu suka rikito daga kan wata gada.
  • A shekara ta 2004, an sake fuskantar irin wannan hatsari a lokacin aikin Hajji a Muna, inda mutane 251 suka halaka, amma a lokacin hukumomi sun ce, kutse wasu suka yi, suka shiga wurin jifan shaidan ba tare da izinin yin hakan ba.
  • A shekara ta 2006, mahajjata 364 sun mutu a lokacin aikin Hajji, kuma lamarin ya auku ne sakamakon wata hatsaniya a gadar Jamarat, sakamakon hatsarin mota da ya haddasa turmutsutsu.

Kafin a soma aikin Hajjin banan, maniyyata 107 ne suka rasu a wani hatsari a Masallacin Harami na Makka.