Kotun Kenya ta umurci malamai su koma aiki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Makarantun gwamnati sun kasance a rufe

Kotu a Kenya ta umurci malaman makarantun gwamnati sun janye yajin aikin da suka shafe wata guda suna yi.

Kotu ta ce malaman su koma bakin aiki ba tare da bata lokaci ba.

Haka kuma kotun ta bukaci kungiyar malamai da kuma bangaren gwamnati su kafa kwamiti domin warware matsalar cikin kwanaki talatin.

Gwamnatin Kenya ta ce ba za ta iya biyan karin albashi na kusan kashi 50 cikin 100 ga malaman ba.

Yara kusan miliyan 12 ne yajin aikin ya shafa a yayin da daukacin makarantun gwamnatin suka kasance a rufe.

Sai dai akwai dai-dai kun makarantun kudi da suke ci gaba da kayar da dalibai.