Wata zai yi Husufi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Husufin wata na faruwa ne a yayin da wata ya shiga tsakanin rana da duniya.

Ana sa rai wata zai yi kusufi a daren yau. Husufin zai shafe hasken watan gaba daya zai fara ne daga misalin karfe 1:00 zuwa karfe 3:00 na daren yau Lahadi.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Dr. Sunusi Mohammed na Hukumar kula da yanayin sararin samaniyar Najeriya a hirar su da BBC.

Jami'in ya bayana cewa kusufin watan wani yanayi ne na Ubangiji kan tsara hakan ya faru daga lokaci zuwa lokaci.

Ya kuma kara da cewa mutane za su iya fita su ganewa idonsu yadda abin zai kasance.

A Najeriya da sauran kasashe makwabta haksen watan ne zai shafe baki daya, a yayin da wasu kasashe na duniya kuwa haske rabi zai kuma koma launi ja.