Sarki Salman ya bayar da umarnin ayi bincike

Image caption Sarki Salman

Sarki Salman na Saudi Arabiya ya bayar da umarnin a gudanar da cikakken bincike dangane da yadda hukumomin kasar ke gudanar da tsare-tsaren ayyukan Hajji bayan mutane fiye da 700 sun mutu a wani tirmutsitsi da aka samu a Mina.

Wasu fiye da 800 kuma sun jikkata.

Wannan ne iftila'i mafi muni da ya afku a lokacin aikin hajj a cikin shekaru 25.

A cikin wani jawabi da ya yi ta kafar talbijin, sarkin ya kuma mika sakon ta'aziyyar sa ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su.

Sarkin ya ce dangane da wannan iftla'i da ya afku, mun bayar da umarni ga hukumomin da alhakin ya rataya a wuyansu da su gudanar da bincke tare da kawo mana sakamakon binciken ba tare da bata lokaci ba.