Hadarin Saudiyya kaddara ce daga Allah

Babban Limamin Saudiyya Sheikh Abdul'aziz bin Abdullah Hakkin mallakar hoto SAUDI PRESS AGENCY
Image caption Babban Limamin Saudiyya Sheikh Abdul'aziz bin Abdullah

Babban limamin na Saudiyya Sheikh Abdul'aziz bin Abdullah al Sheikh ya kuma tsame Yarima Mohammed bin Nayef wanda shine ke kula da ayyukan hajjin baki daya inda ya shaida masa cewa kaddara ba'a iya hana aukuwarta.

Iran da wasu kasashe wadanda alhazan su suka rasu a hadarin sun soki hukumomin Saudiyya kan yadda suka aiwatar da matakan kariya.

Babban mai gabatar da kara na kasar Iran Hojjat ol Eslam Seyyed Ebrahim Ra'isi ya yi kiran gurfanar da 'yan gidan sarautar Saudiyya a gaban kotu domin fuskantar shari'a.

Mutane 769 aka tabbatar da mutuwar su a hadarin kawo yanzu.