"'Yan Nijar 22 ne suka mutu a Mina"

Image caption Kasashe da dama suna ta bayyana adadin mutanen da suka rasa rayukansu a hatsarin

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da mutuwar 'yan kasar 22 a turmitsitsin da ya auku wajen aiki hajji a Saudi Arabia.

Gwamnatin kasar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar, inda ta kara da cewa mutane da da ma kuma sun jikkata.

Sanarwar ta kuma ce akwai mutane da yawa kuma da har yanzu ba a ji duriyarsu ba, kuma ba ta tantance ko sun mutu ba ko kuma suna raye.

Gwamnatin ta kara da cewa wadannan bayanai na wucin gadi ne kuma ta tabbatar da hakan ne bayan ta samu bayanai daga bakin Ministan harkokin cikin gida daga Saudiyya.

Tuni gwamnatin ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku daga gobe Litinin, tare da kafa wasu kwamitoci da za su ci gaba da bin lamarin sau-da-kafa.