An tabbatar da rasuwar alhazan Nigeria 54

Image caption Mahajjatan Najeriya

Hukumar alhazan Najeriya ta ce Mahajjatan kasar hamsin da hudu ne su ka mutu a sakamakon turmutsitsin da aka samu a wajen jifan Shedan a Makkah.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Malam Uba Mana ya shaida wa BBC cewa wasu mahajjatan saba'in da bakwai kuma sun samu raunuka, yayin da wasu kuma ba a kai ga gano inda suke ba.

Malam Uba Mana ya ce daga cikin jihohin da suka rasa Alhazan su akwai Bauchi, Borno, Cross River, Jigawa, Kebbi, Nasarawa, Yobe, Taraba da dai sauran su.

Jami'in ya ce yanzu haka hukumar ta kafa wasu kwamitoci guda biyu -- na farko zai ci gaba da neman mahajjatan da ba a gansu ba, yayin da na biyun kuma zai kula da iyalan wadanda suka rasa rayukan su ta yadda za a rinka sanar da iyalansu halin da ake ciki.

Kasashen Alhazan da suka rasu;

 • Iran: 169
 • Morocco: 87
 • Egypt: 55
 • Nigeria: 54
 • Indonesia: 41
 • India: 35
 • Cameroon: akalla 20
 • Niger: 22
 • Pakistan: 18
 • Ivory Coast: 14 , 77 sun bace
 • Chad: 11
 • Somalia: 8
 • Algeria: 8
 • Senegal: 5
 • Libya: 4
 • Tanzania: 4
 • Kenya: 3
 • Burkina Faso: 1
 • Burundi: 1
 • Netherlands: 1
 • Tunisia: 1
 • Benin: ba a san adadin ba