Ana ci gaba da tashin hankali a Bangui

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shekaru biyu ana zaman dar-dar a Bangui

Tashin hankali ya ci gaba da wakana a tsakanin bangarori biyu masu gaba da juna a Jamhuriyar tsakiyar Afrika duk da dokar hana fitan dare a birnin Bangui da aka kafa.

Gwamnati na zargin 'yan adawa da tayar da wannan tashin hankali domin kada a gudanar da zabe kamar yadda aka shirya gabannin karshen wannan shekara.

A yanzu haka dai ana kiyasta mutane 35 ne suka hallaka a tashin hankalin da aka soma tun a karshen mako a yayin da kusan 40 ne suka jikkata.

An ci gaba da jin karar harbe-harbe da kuma rushe-rushen gidaje da kantuna a birnin Bangui hadi da kwasar ganima a cikin dare.

Ofishoshin wasu kungiyoyi masu zaman kansu da kuma na majalisar dinkin duniya basu tsira ba, kamar Hukumar samar da abinci da kuma Hukumar ayyukan jinkai.

A yanzu haka dai, bangaren da ke adawa da gwamnati ya bukaci Shugabar kasar ta wucin gadi Catherine Samba Panza da ta yi murabus.

Tun watan maris na shekara ta 2013, lokacin da aka hambarar da shugaban kasa Francois Bozize, Jamhuriyar tsakiyar Afrika ta fada a cikin wani rikici na addini da kuma na kabilanci, mafi muni tun lokacin da ta samu 'yancin kai a shekara ta 1960.