'Yan Kamaru 21 ne suka rasu a Mina

Image caption Gwamnatin Kamaru ta ce mahajjatanta 77 suka jikkata.

Hukumomi a kasar Kamaru sun ce 'yan kasar 21ne suka rasu a turereniyar da aka yi a lokacin jifan Shedan a Mina da ke Saudiyya ranar Alhamis.

Ma'aikatar kula da harkokin cikin gidan Kamaru, wacce ta bayar da wannan sanarwa, ta kara da cewa 'yan kasarta 77 ne suka jikkata sakamakon hatsarin.

A cewar ma'aikatar, Shugaba Paul Biya ya bai wa ofishin jakadancin Kamaru da ke Sa'udiyya umarnin kulawa da mutanen da suka jikkata.

Kazalika, hukumomin sun ce ana ci gaba da neman wasu maniyyata da har yanzu ba a samu labarinsu ba.

Gwamnatin ta Kamaru ta ce nan ba da dadewa ba za ta bayar da cikakkun bayanai game da 'yan kasarta da wannan lamari ya rutsa da su.

A bana, maniyyatan Kamaru 4,500 suka je Saudiyya domin gabatar da aikin Hajji daga cikin mutane sama da 10,000 da suka mika bukatunsu.