Ana zanga-zanga a Congo

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Denis Sassou Nguesso

Dubban mutane a kasar Congo ne ke yin zanga-zanga a Brazzaville, babban birnin kasar, domin nuna kin amincewa da shirin da Shugaba Denis Sassou Nguesso ke yi na yin tazarce karo na uku.

Wannan ita ce zanga-zanga mafi girma da aka yi a kasar tun bayan komawar Shugaba Sassaou kan mulki a shekarar 1997.

Wasu ganau sun bayyana cewa tsawon yawan mutanen da ke zanga-zangar ya kai kilomita guda.

A makon jiya ne Shugaba Sassou ya sanar da shirin kuri'ar raba-gardama a kan sauya tsarin mulkin kasar, don hakan ya ba shi damar sake tsayawa takara.