'Yan Nigeria na dakon sunayen ministoci

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Buhari ya ce masu tabo ba za su shiga gwamnatinsa ba

Miliyoyin 'yan Nigeria na dakon sunayen da shugaban kasar zai mika wa majalisar dattijan kasar a matsayin wadanda yake son ya nada ministoci.

Watanni hudu kenan da rantsar shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa, kuma ya tabbatar da cewar alkawarinsa na nan daram na bayyana sunayen ministocinsa a watan Satumba

Wannan batu na ministoci dai batu ne da yake ci gaba da jan-hankulan 'yan kasar na ganin irin mutanen da Shugaban zai yi tafiya da su a gwamnatinsa.

'Yan Nigeria a shafukan zumunta na zamani dai suna ta bayyana ra'ayoyinsu da kuma shawarwarinsu ga shugaban kasar a kan wadanda suke son ganin shugaba Buhari ya nada a matsayin ministocinsa.

Shugaba Buhari dai na halartar babban taron Majalisar dinkin duniya a birnin New York inda ya kalubalanci shugabannin duniya su kawar da talauci da kuma cututtuka daga doron kasa.

Ana sa ran shugaban kasar zai koma Nigeria a ranar 29 ga watan Satumba.