Ta'asar da aka yi a Sudan ta Kudu

Image caption Garin Nyl, dake Jihar Unity, na daya daga cikin yankunan da 'yan tawaye suka rike

An karya dokar yaki tun da dadewa a Sudan ta Kudu, amma kuma tashe-tashen hankula da ake yi a kan fareren hula a baya-bayan nan ya haifar da wani sabon rashin imani.

An zargi gwamnatin kasar da sojojin 'yan tawaye da tafka ta'asa a watanni 21 na yaki, amma kuma labaran da wadanda suka tsira daga tashe-tashen hankula a watannin baya-bayan nan suke bayarwa na da ban tsoro.

Sun bayar da labarin mata da yara wadanda aka yi wa fyade ko aka yi garkuwa da su, da kuma iyalan da aka kona a gidajensu da kuma labarin akalla yaro daya wanda aka rataye a jikin bishiya.

Rashin dabbobi a garin Leer da ke jihaer Unity, da kuma gonaki da filaye da rugage, shaida ce ta abin da ke nuna alamun halakar da garin.

Leer, shi ne garin shugaban 'yan tawaye Reik Machar, kuma a da a nan ne mafi yawancin rundunar soji magoya bayansa suke a lokacin da sojojin suka rabu.

A yanzu kusan ba komai a garin, saboda dubban mutane sun tarwatse zuwa cikin garin Nile mai laka da kuma wasu sansanonin 'yan gudun hijira da suke cike makil.

'Tsaka mai wuya'

*Me ya sa Amurka ta damu da Sudan ta Kudu ?

A Disambar shekarar 2013, rikice-rikicen a babban birnin Sudan ta Kudu watau Juba, ya bazu a sassa daban-daban na kasar, wanda hakan ya haifar da rarrabuwar sojoji ta kabilanci, wanda kuma mafi yawancin sojojin 'yan tawayen 'yan kabilar Nuer.

Yayin da gwamnatin Sudan ta Kudu ta ce wani yunkuri ne na juyin mulki, 'yan tawayen sun ce wata makarkashiya ce ta siyasa a kan jam'iyyar adawa.

Sai dai kuma babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da abin da ya jawo fadan, amma kuma babu shakka miliyoyin mutane sun rasa muhallansu kuma wasu miliyoyin suna fama da cututtuka da yunwa.

Nyaguar Nhial ta ce ita da iyalan ta sun gudu daga wajen fadan zuwa wurin ciyayi da bakin ruwa, ta ce sun shafe kwananki da kusan dukkanin jikinsu daga wuya zuwa kafafuwansu a cikin ruwa su da yaransu a kan tabarmar kaba.

Ta ce "duk da haka, sojojin suna harbi zuwa cikin ruwan, inda ta ke bayanin yadda suka jira sai dare yayi sa'anan su fito fili su yi bacci sai su koma cikin ruwa da garin ya waye."

'Gudun hijira'

Sun shafe watanni biyu suna cikin wannan halin, sai dai kuma da yunwa ta addabe su sai suka je neman taimako a sassanin 'yan gudun hijiran.

Ba kasafai ake iya rarrabewa ba tsakanin rikice-rikicen kabilancin ba, kuma ana zargin kabilar Bul- Nuer da kuma matasansu sojojin sa-kai da hada kai da dakarun gwamnatin wajen kai hare-haren a jihar Unity.

Sudan ta Kudu ta na fama da 'yan ta'adar masu satar shanu, sakmakon hakan yanzu babu shanu masu yawa a garin Leer, sai a yankin Bul-Nuer inda ake da tarinsu a yanzu.

A yayin da rikici ba wani sabon abu bane, an saba ka'idoji sannan kuma yaki ya lalata inda a da ya ke da kwanciyar hankali ga mata da yara su fake.

Duk wani sabon zuwa sansanin a Bentu na Majalissar dinkin duniya yana da mummunar labari da zai iya bayarwa - shi ya sa suka je sansanin.

Shi yasa kuma yawan mutane ya nunka sau uku a 'yan watanni kuma cunkoson ya yi muni ta inda mutane ke fama cutar cizon sauro kuma yara na mutuwa a sanadiyar tamowa.

Wata mata 'yar Sudan ta Kudun wacce ta ke aiki da Asusun kula da kananan yara ta majalissar dinkin duniya, wacce bata so a bayyana sunan ta ba, tana tattara shaidu daga wadanda suka iso sansanin.

Abin da ta gano ya karfafafa rahoton da majalissar dinkin duniya da kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch da kuma rahoton da Tarayyar Afrika ta fitar na azabtarwa.

Ta ce "Da akwai yara da dama da aka kashe. Sun shaidi kashe mata kuma sun gani da idanunsu, a yankunan da suka zauna, an yi wa mata da yara da dama fyade wasu kuma aka yi garkuwa da su, sun tafi da su ne tare da shanun."