'Babban watan da ya zo daidai da Husufi'

Image caption Husufi a kasar Belgium

Mutane a duniya sun taru domin ganin wani abun mamaki, inda husufi ya tarar da babban wata.

Babban wata yana fitowa ne lokacin da ya matso kusa da duniya, wato sai a hango shi lokacin da ya fi sararin samaniya girma.

An sha ganin husufi wanda ke sa kalar wata ta komo ja, a garuruwan arewa da kudancin Amurka da yammacin Afrika da ma yammacin Turai.

Wannan yanayi na ban mamaki ya yi bullowar karshe a shekarar 1982, kuma ba za a sake ganin sa ba sai shekara 2033, duk da cewar akwai jayayya a kan asalin bayanin babban wata.

'Yan sama jannati da ke kasashen yamma a arewacin Amurka da Turai da Afrika da gabas ta tsakiya da kuma Afrika ta kudu sun gano rabin husufi.

Image caption Husufi a garin Glastonbury da ke yammacin Ingila

Masu kallo a Biritaniya sun ga yadda wata ya wuce inuwar duniya da safiyar Litinin, amma a arewa da kudancin Amurka sun gan shi ne ranar Lahadi da yamma.

Bayanai kan Husufi

  • Girman wata na karuwa saboda kusancinsa da duniya, inda babban watan ke da kimanin girman kaso 7 zuwa 8 cikin 100, fiye da girman taurari.
  • Wata na shigen yanayi da launin karfen da ya zagwanye, hakan ma ya sa ake masa lakabi da 'Blood Moon' watau 'Wata mai kama da jini', saboda duniya tana watso kalar shudi ne, a yanayinta fiye da ja, shi ne dalilin da ya sa jan ke fadawa wurin wata.
  • A lokacin husufi, wata na zama gaban taurarin jerin kifaye.

A kan sami husufin da ya mamaye ko'ina, inda duniya da rana da wata suka jeru layi daya kuma gefe da gefe.

Image caption Babban wata a birnin Geneva

Masu duba a duniya kuma na iya hango kalar wata na canzawa duba ga sauyin yanayi. Daga kalar jar kasa ko kalar karfen da ya zagwanye ko kalar jini, ko ma kalar toka.

Dr. Robert Massey, mataimakin shugaban kungiyar 'yan sama jannati, ya shaidawa BBC cewa, husufi wani abin ban mamaki ne mai ban sha'awa.

Ya yi bayanin cewa bai kamata a yi ta samun rudani a kan babban wata da ainihin wata ba, domin duk daya suke, watan na matsowa kusa da duniya ne yasa ake ganin girman sa.

Image caption Husufi a Las Vegas

Husufin ya soma da misalin karfe 12, lokacin da wata ya shige inuwar duniya mara kauri, wadda aka fi sani da 'Penumbra' sannan kuma kalarsa ta canza zuwa kalar kwaiduwa, daga bisani da misalin karfe 2:11, watan ya kuma shige kakkaurar inuwar duniya, wanda ake cewa 'Umbra', baki daya.

An samu mafi girman husufi da misalin karfe 2:47, lokacin da wata ya fi shigewa tsakiyar 'Umbra' daga nan kuma husufin ya kare da karfe 5:22.

Kungiyar 'yan sama jannati ta tabbatar da cewa ana iya kallon husufin wata da idanu, ba kamar husufin rana ba.