Rikici a kusa da masallacin Kudus

Image caption Matasan Falasdinawa sun fafata da jami'an tsaron Isra'ila

Rikici ya barke tsakanin jami'an tsaron Isra'ila da Falasdinawa a kewayen masallacin al-aqsa da ke birnin Kudus.

'Yan sanda sun harba hayaki mai sa kwalla kan matasa wadanda ke jifa da duwatsu da bama-baman fetur.

Masallacin wanda ke gabashin birnin Kudus inda Isra'ila ta mamaye na da muhimmanci ga duka Musulmai da Yahudawa.

Yawanci dai a kan samu hatsaniya a wajan, amma abin ya yi kamari musamman a 'yan makonnin nan.

Kuma musabbabin hakan shi ne Falasdinawa na zargin cewa Isra'ila za ta yi wasu sauye-sauye kan yadda ake tafiyar da wajen, zargin da Isra'ila ta musanta.