Jamus ta soma bincike kan Volkswagen

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Winterkorn na ciki tsaka mai wuya

Masu shigar da kara a Jamus sun fara gudanar da bincike kan tsohon shugaban kamfanin kera motoci na Volkswagen, Martin Winterkorn.

A makon da ya gabata ne ya yi murabus, sakamakon wata badakala da ta dabaibaye kamfanin na magudin gwajin gurbataccen hayakin da motocin da ke amfani da man dizel ke fitarwa.

Binciken zai mai da hankali a kan zarge-zargen ha'inci a sayar da motocin.

Mr Winterkorn dai ya musanta masaniya kan abun da ke faruwa.

A wani labarin kuma, hukumar sufuri ta Jamus ta bai wa kamfanin Volkswagen nan da ranar bakwai ga wata Oktoba, da ya mika tsare-tsaren da zai yi na saka motocinsa da ke amfani da man dizel cikin tsarin dokar kasar.