Kawancen Boko Haram da IS ba alheri ba ne'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Buhari ya ce za su samu galaba a kan Boko Haram

Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida wa shugabanin duniya a babban taron majalisar dinkin duniya da ake yi a birnin New York, cewar hare-haren Boko Haram sun karu tun bayan da suka yi mubaya'a ga kungiyar IS.

Sai dai ya ce gwamnatinsa tare da hadin gwiwar makwabtan kasashe za ta ci gaba da ayyukan soji domin murkushe kungiyar.

"Bayan Boko Haram sun yi mubaya'a da ga IS shi ne yasa kisan mutane da dama da fille kawunan mutane a irin salon kungiyar IS a bainar jama'a ya karu," in ji Buhari.

Ya kara da cewar "Mun lura cewar masu sakawa mutane tsatstsaurar ra'ayi suna ba da kulawa ta musamma ga yankin Afrika Kudu da hamadar sahara."

Buhari ya ce "Hakika ya kamata mu kara himma. Ya kamata mu dauki matakan soji, mu kuma kara tsaro a kan iyakokinmu. Akwai bukatar musayar bayanan sirri da kuma sa ido sosai."

Shugaba Buhari ya bai wa rundunar sojin kasar wa'adin zuwa karshen wannan shekarar domin kawar da Boko Haram.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun hadin gwiwa suna kokarin kawar da Boko Haram

A cikin watanni hudu da soma mulkin Buhari, kungiyar Boko Haram ta hallaka fiye da mutum 1,000.