Burkina Faso: Sojoji sun kwace barikin soji

Janarar Gilbert Deindere
Image caption Janarar Gilbert Deindere

Mahukunta masu rikon kwarya a kasar Burkina Faso sun ce sojoji sun kwace ikon barikin soji da dakarun da ke gadin shugaban kasar suke zaune wadanda suka yi juyin mulki a farkon watan nan na Satumba.

Sojoji sun kaddamar da farmaki a sansanin, da ke Ouagadougou babban birnin kasar, bayan da masu gadin shugaban kasa suka ki mika wuya.

An dai rika jin karar harbe-harben bindigogi.

Sai dai kawo yanzu ba bu cikakken bayani a kan wurin da jagoran juyin mulkin yake watau janar Diendere.

Tun farko dai janar Diendere ya yi kira ga masu tsaron shugaban kasa a kan su ajiye makamansu.

Hafsan sojin kasar ya ce mutane 300 ne suka mika wuya.