Sabon rikici ya barke a Burundi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Pierre Nkurunziza

Rikice-rikicen siyasa sun sake barkewa a Bujumbura, baban birnin Burundi tun da shugaba Pierre Nkurunziza ya yanke shawarar ci gaba da mulkin kasar a karo na uku a watan Afrilun shekarar 2015.

Jama'a na ci gaba da kasan cewa cikin zaman dar-dar a kullum saboda rashin tabbas a kan makomar siyasar kasar.

Kaddamar da hari da makamai ya zama ruwan dare a cikin Bujumbura kuma a halin da ake ciki ana ta samun rahotannin sojojin da suke tserewa daga kasar.

Majalisar dinkin duniya ta ce an kashe sama da mutane dari kuma ana tsare da sama da dari yayin da 'yan Burundin sama da 100,000 suka fice daga cikin kasar.