Bangui: An sanya dokar hana fitar dare

Shugabar jamhuriyar tsakiyar Afrika Catherine Samba Panza
Image caption Shugabar jamhuriyar tsakiyar Afrika Catherine Samba Panza

Hukumomi a Jamhuriyar tsakiyar Afrika sun ce an sanya dokar hana fitar dare a Bangui babban birnin kasar, bayan kwanaki da aka kwashe ana fada tsakanin kungiyoyin Kiristoci da Musulmai.

Ministan cikin gida na kasar Modibo Bachir Walidou, ya shaida wa BBC cewa gwamnati ta shawo kan lamarin, sai dai kuma ana zaman dar-dar, yayin da wasu rahotanni ke cewa har yanzu ana ci gaba da gwabza fada.

Kungiyoyin sun yi fito na fito ne bayan da aka kashe wani direban tasi wanda Musulmi ne a birnin Bangui a ranar Asabar.

Mutane akalla 36 ne aka kashe a tashin hankalin kuma a cewar Majalisar Dinkin Duniya, lamarin ya tilastawa mutane kusan 30,000 barin gidajensu.

Tun bayan da kungiyar 'yan tawaye da galibi Musulmi ne da ake kira Seleka suka kwace iko a watan Maris na shekara ta 2013, Jamhuriyar tsakiyar Afrika ke fuskantar tashe-tashen hankula.

Sai dai bayan da aka kawar da kungiyar ta Seleke ne aka soma kai wa Musulmi harin ramuwar gayya lamarin da kuma ya sa duban Musulmai barin gidajensu.