'Ba a ji ɗuriyar alhazan Nigeria 244 ba'

Hukumomin Saudiyya sun ce mutane fiye da 700 ne suka rasu
Bayanan hoto,

Hukumomin Saudiyya sun ce mutane fiye da 700 ne suka rasu

Hukumar kula da aikin hajji ta Nigeria ta tabbatar da rasuwar alhazai 64 sakamakon turmutsitsin da aka samu a hanyar zuwa jifan shaidan a Muna.

Kakakin hukumar Uba Mana, a hirarsa da BBC ya ce akwai kuma mutane 71 da suka samu raunuka wadanda ke samun kulawa a asibitoci a Saudiyyar.

A cewarsa, kawo yanzu akwai alhazai 244 da ba a san inda suke ba kuma ba a ji duriyarsu ba tun bayan da aka samu hadarin.

Hakan na zuwa ne bayan da shugaba Muhammadu Buhari, ya bukaci hukumar aikin Hajji ta Nigeria da Ofishin Jakadancin kasar a Saudiyya da su gaggauta tantance 'yan kasar da wannan lamari ya shafa, domin a sanar da danginsu.

Rahotanni dai sun nuna cewar yawan alhazan da suka rasu a hadarin da ya auku ranar Alhamis ya haura mutane 1,000 daya.

Alkaluman da hukumomin Saudiyya suka fara fitarwa dai na cewa sama da mutane 700 ne suka mutu.